Feb 13, 2019 12:40 UTC
  • Nijar : An Kafa Dokar Hana Fitar Dare A Tillaberi

A wani mataki na karfafa matakan tsaro hukumomi a jihar Tillaberi sun sanar da kafa dokar hana fitar dare.

Dokar ta tanani hana zurga zurga ga masu babur ko moto, da motoci daga karfe 7 : 00 na yamma har zuwa 6:00 na safe.

Sai kuma haramta fita ga masu tafiya a kafa, daga karfe 10 : 00 na dare har zuwa 6 : 00 na safe.

Sanarwa da hukumomin birnin suka sanya wa hannu ta kuma baiwa jami'an tsaron damar gudanar da samame da bincike a duk inda ya kamata, ba dare ba rana.

Tags