Feb 14, 2019 11:14 UTC
  • An Soki Tsoma Bakin Da Faransa Take Yi A Harkokin Cikin Gidan Kasar Chadi

Tashar talabijin din Rashatody mai zaman kanta ta bayyana hare-haren da jiragen yakin Faransa su ka kai a kasar Chadi da zummar kare gwamnatin shugaba Idris Deby da cewa ba ya bisa doka

Rahoton ya kuma yi watsi da maganganun ministocin tsaro da na harkokin waje na kasar Faransa da su ka kare harin da jiragen yakin kasar su ka kai wa masu adawa da gwamnatin Idris Deby tare da bayyana shi a matsayin wanda ba ya bisa doka.

Ministan harkokin waje na kasar Faransa Jean Le Drian ya fada a ranar Litinin din da ta gabata cewa; Harin da aka kai wa masu adawa da gwamnatin shugaba Idris Deby yana karkashin amsa kiran neman taimako da gwmanati da kuma majalisar kasar Chadi su ka yi ne

A cikin kasar Chadi ma shugaban jam'iyyar 'Yanci da Raya kasa, Muhammad Ahmad Alabo ya ce; Tsoma bakin da kasar Faransa ta yi a harkokin cikin gidan kasar Chadi yana cin karo da dokokin kasa da kasa.

A ranakun 5 da 6 ga watan Febrairu ne dai jiragen yakin kasar Chadi su ka kai hari akan wasu motocin 'yan tawaye 40 da su ka shiga kasar Chadi daga Libya

Tags