Feb 15, 2019 05:09 UTC
  • Nijar : Ana Ci Gaba Da Neman Mutanen Da Suka Bace A Kifewar Kwale-kwale

Rahotanni daga Jamhuriya Nijar, na cewa, ana ci gaba da neman wasu mutane da suka bata bayan da wani kwale-kwale dauke da mutane kimanin 100 ya kife a kogin Nijar a ranar Laraba data gabata.

Bayanai sun nuna cewa kwale kwalen ya taso ne daga kauyen Karimama na Jamhuriya Benin zuwa kasuwar Ouna dake kasar ta Nijar, a yayin da ya kife kimanin mita 200 kafin ya isa inda za ya.

An dai yi nasara cewa mutum 62 zuwa 64 daga cikin mutanen da hadarin kwale kwalen ya rusa dasu, a yayin da ake ci gaba da neman sauren.

Wasu majiyoyi daga yankin sun ce kimanin mutum arba'in ne ake ci gaba da nema, har zuwa lokacin da jami'an tsaro da suka hada da 'yan sanda da kuma na ruwa da masinta suka dakatar da aikin neman mutanen wadanda akasarinsu 'yan Benin ne saboda shigar dare.

Tuni dai aka riga aka kaddamar da bincike daga bangarori biyu na inda kwale kwalen ya taso da kuma inda za ya, domin gano musabbanin hadarin, a daidai kuma lokacin da ake sa ran matukin kwale kwalen da kuma mai kwalen kwalen zasu gurfana gaban mai shigar da kara na yankin.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da ake fuskantar irin wannan hadarin kwale kwale a yankin ba, inda a shekaru biyu da suka gabata ma irin hakan ta taba faruwa.

Tags