Feb 15, 2019 19:20 UTC
  • Jami'an Tsaron Kasar Morocco Sun Sami Nasarar Wargaza Wata Kungiyar Yan Ta'adda.

Ma'aikatar cikin gida na kasar Morocco ta bada sanarwan cewa ta sami nasarar wargaza wani shirin hare0haren ta'addanci a yammacin kasar.

Tashar talabijinn ta Sky News ta bayyana cewa gungun yan ta'addan ta kunshi mutane 5 wadanda suke tabbatar da cewa suna cikin kungiyan yan ta'adda ta Daesh, sun shirya kai hare-haren ta'addanci a yammacin kasar ta Morocco, amma binciken da jami'an tsaro suka yi gid-gida a yankin ya sa suka gano mabiyarsu, sannan suka gani wasu shaidu wadanda suka tabbatar da cewa su yayan kungiyar yan ta'adda ta Daesh ne. 

An gano wasu rubutun hannu wanda ya nuna dangnatakarsu da kungiyar ta Daesh ta ke kasashe Iraqi da Syriya, sannan akwai makamai na gargajiya, da kuma shaida da sune kirin mutane zuwa ga tashin hankala a hannunsu. 

A cikin yan kwanakinn da suka gabata ma gwamnatin kasar ta Morocco ta kama mutane 3 yan kasara Faransa wadanda suke tallafawa yan ta'adda kudade.

Tags