Feb 16, 2019 04:00 UTC

Hukumar zaben Najeriya INEC ta sanar da dage zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a yau Asabar a fadin kasar, sanarwar da ta zo 'yan sa'oi kafin fara gudanar da zaben.

Shafin jaridar Sahara Reporters ya bayar da rahoton cewa, da jijjifin safiyar yau ne shugaban hukumar zaben ta Najeriya Farfesa Mahmoood Yakubu ya sanar da cewa, hukumar ta INEC ta dage gudanar da zaben da aka shirya gudanarwa a yau Asabar, bayan wani zama da ta gudanar a daren jiya Juma'a, inda ta yanke wannan shawara.

Bayanin ya ce an dage gudanar da zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a yau har zuwa ranar 23 ga wannan wata na Fabrairu da muke ciki, wanda zai gudana tare da na 'yan majalisar dokokin kasar.

Sai kuma zaben gwamnoni tare da na 'yan majalisun jahohi zai gudana a ranar 9 ga watan Maris mai kamawa.

Bayanin ya kara da cewa, hukumar ta INEC ta dauki wannan mataki ne saboda wasu 'yan matsaloli da ta fusanta da sua danganci shirye-shirye zaben, da hakan ya hada da rashin kai kayan zabe cikin lokaci a wasu yankuna na kasar, duk kuwa da cewa kafin wanann lokaci hukumar ta sanar da cewa ta shirya tsaf domin gudanar da zabukan.

Manyan jam'iyyun siyasa biyu na kasar APC mai mulki da kuma PDP mai adawa sun yi Allawadai da matakin.

 

Za a iya sauraren bayanin na Farfesa Mahmood Yakubu da ya yi dazu-dazun nan kan wannan batu idan aka matsa wannan hoto

 

Tags