Feb 17, 2019 10:37 UTC
  • An Hallaka Mayakan (IS) Bakwai A Masar

Rundinar sojin kasar Masar, ta sanar da hallaka mayakan kungiyar (IS), guda bakwai, a yayin da suka kai hari kan wani shingen bincike na soji a arewacin yankin Sinai.

Da yake sanar da hakan Wata sanarwa da kakakin rundinar sojin kasar ta Masar, Tamer el-Refai, ya fitar, ta ce akwai sojojij kasar ta Masar 15 da suka rasa rayukansu ko suka raunana a harin. 

Sojojin Masar dai sun jima suna kai hari kan mayakan na IS a wannan yankin na Sinai.

Kan yawaitar hare haren mayakan na IS ne ma, sojojin kasar ta Masar suka kaddamar da wani gagarimin farmaki a bara na kakkabe yankin daga mayakan na IS, da kuma tsarkake kasar daga duk wata barazanar ta'addanci.

Tags