Feb 20, 2019 17:54 UTC
  • An Kashe Fararen Hula 14 A Najeriya

Majiyar tsaro a Najeriya ta sanar da cewa; Kungiyar Boko Haram ce ta yi wa fararen hular kisan gilla a wani yanki da ke kusa da Maiduguri a jahar Borno

Kamfanin dillancin labarun Faransa wanda ya dauki labarin ya kuma ce; A cikin watan Janairu da ya shude ma 'yan kungiyar ta Boko haram sun kai wani harin a wani kauye da yake kusa da Maiduguri tare da kashe manoma da suke cikin gonakinsu.

'Yan ta'addar kungiyar Boko haram sun sha kai hare-hare akan mutanen karkara musamman manoma da kuma makiyaya suna masu zarginsu da yi wa jami'an tsaron kasar leken asiri

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin kawo karshen kungiyar ta Boko haram a lokuta daban-daban, sai dai har yanzu kungiyar tana ci gaba da kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin kasar

A cikin watannin bayan nan hare-haren kungiyar ta boko haram sun tsananta tare da kashe sojoji da kuma fararen hula.

A shekarar 2009 ne dai kungiyar ta 'yan ta'adda ta fara kai hare-hare a cikin yankin arewa maso gabashin Najeriya wnada ya zuwa yanzu ya ci rayukan fiye da mutane 20,000.

Bugu da kari hare-haren kungiyar ta Boko haram ya tilastawa fiye da mutane miliyan 2 yin hijira a cikin gida da kuma kasashen makwabta.

Kungiyar tana a matsayin brazanar tsaro ga Najeriya da kuma kashashen Nijar, Kamaru, da Chadi

 

Tags