Feb 22, 2019 12:30 UTC

Magoya bayan Harkar Musulunci a Najeriya suna ci gaba da yin kira ga gwamnatin tarayyar kasar da ta saki Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Rahotanni daga tarayyar Najeriya na nuni da cewa, magoya bayan Harkar Musulunci karashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky suna ci gaba da gudanar da jerin gwano musamman a birnin Abuja, domin yin kira ga gwamnatin kasar kan ta sake shi.

Harkar Muslucni ta bayyana ci gaba da tsare Sheikh  Ibrahim Zakzaky da cewa yana matsayin yin watsi da umarnin kotu ne, ganin yadda kotun tarayya ta bayar da umarnin sakin shi a lokutan baya.

Gwamnati dai ta ce tana ci gaba da tsare Sheikh Zakzaky bisa wasu tuhumce-tuhumce, duk kuwa da cewa an mayar da batun nasa ga wata kotu da ke Kaduna, bayan da gwamnatin Kaduna ta shigar da kara a kansa.

Daga cikin tuhumce-tuhumcen da gwamnatin Kaduna ta yi a kan Malamin har da zargin tayar da hankali, da kuma kisan soja guda a lokacin da sojoji suka kai farmaki a gidansa a karshen shekara ta 2015.

Harkar musulucni da kungiyoyin kare hakkin bil adama na ciki da wajen Najeriya sun ce sojoji sun kashe mutane masu tarin yawa a lokacin da suka kai hari kan Husainiyyar bakiyatullah da kuma gidan sheikh Zakzaky a Gyallesu Zaria,  tun daga ranar 12 ga watan Disamban 2015 har zuwa 14 ga wata, inda gwamnatin Kaduna ta yi ikirarin cewa ta bizne gawawwakin mutane 347, yayin da majiyoyin Harkar musulucni suka bayar da bayanai kan cewa sojojin sun kashe fiye da mutane 1000 wadanda aka fitar da sunayensu, tare da kame wasu masu yawa.

A kan wannan batu mun ji ta bakin Malam Aliyu Khalil daya daga cikin magoya bayan harkar Musulunci, kan dalilan da suka sanya suke ci gaba da gudanar da wanann zanga-zanga ta neman a saki Sheikh Zakzaky. Ga abin da yake cewa: