Feb 22, 2019 19:10 UTC
  • Sojojin Faransa Sun Kashe Wani Jigo A Wata Kungiyar Yan Ta'adda A Kasar Mali.

Gwamnatin kasar Faransa ta bada sanarwan cewa sojojinta sun kashe wani fitaccen dan ta'adda a yankin Sahel a kasar Mali.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto ministan tsaron kasar Faransa yana fadar haka a yau Jumma'a a birnin Paris babban birnin kasar. Florence Parly ya kara da cewa Yahia Abu Hamman shi ne mataimakin komandan kungiyar yan ta'adda wacce ake kira Jama'at Nusratul Islam wal-muslimin (JNIM) wacce kuma take karkashin kungiyar Alqaeda. Kungiyar tana gudanar da ayyukan ta'addanci a kasashen yammacin Afrika. 

Har'ila yau ita ce ta dauki alhakin wani harin ta'addancin da aka kai a kasar Burkina Faso a baya-bayan nan. Banda haka mayakan kungiyar sun yi kokarin rikita zabubbuka da aka gudanar a kasar Mali a shekarar da ta gabata. 

Ministan harkokin wajen na kasar Faransa Florence Parly, ya ce sojojin kasar Faransa sun gano Hamman a lokacinda yake tafiya da tawagarsa a arewacin birnin Timbuktu daga arewacin kasar ta Mali a ranar 21 ga watan Febrerun da muke ciki. Ya ce sojojin sun kashe shi da wasu wadanda suke tare da shi ne a wani sumamen da suka kaiwa tawagarsa ta sama da kasa. 

Daga karshe ministan ya bayyana cewa kashe irin wadanna manya-manyan yan ta'adda zai taimaka wajen wargaza kungiyarsu. 

 

Tags