Feb 23, 2019 16:27 UTC
  • Ana Samun Galaba A Yaki Da Ta'addanci A Yankin Sahel_Faransa

Firaministan Faransa, Edouard Philippe, ya bayyana cewa ana samun galaba a yakin da ake da mayakan dake ikirari da sunan jihadi da kuma matalsar tsaro a yankin sahel.

Mista Philippe, na bayyana hakan ne a yayin ziyarar kwanaki biyu da yake a kasar Mali, inda ya kara da cewa yakin ta'addancin da ake a yankin na sahle na bukatar juriya, kasancewra muna fuskantar yaki mai tsanani ne.

Ziyarar ta firaministan na Faransa na zuwa ne kwana guda bayan sanarwar da rundinar sojin Faransa ta fitar na hallaka wani babban jigo a kungiyar mayakan dake ikirari da sunan jihadi mai alaka da kungiyar Al-Qaïda, dan asalin kasar Aljeriya, Djamel Okacha, wanda ake kira da Yahya Abu El Hamame.

A yayin ziyarar da ya fara jiya Juma'a, a Bamako, shugaban gwamnatin Faransar, zai gana da takwaransa na Mali, Sumeylu Boubèye Maïga, da shugaban kasar Ibrahim Boubakar Keïta.

Daga bisani kuma Firaministan na Faransa zai sanya hannu kan wasu sabbin yarjejeniyoyi na ci gaba da Mali da suka kai na sabar kudi Miliyan 85 Yuro, wanda ya tanadi miliyan 50 na bashi da kuma 35 na tallafi, ta hanyar shirin nan na Faransa na samar da ci gaba AFD.

Ko baya ga hakan kuma Faransa zata kara jaddada kasancewar tawagar sojojinta na rundinar Barkhane, data kunshi sojoji 4,500 a yankin Sahel, wanda kuma suka hada da 2,700 a kasar ta Mali.

Tags