Feb 25, 2019 05:46 UTC
  • An Kashe Sojojin MDD 3 A Kasar Mali

Ma'aikatar tsaro da kare fararen hula a kasar Mali ta bada sanarwan cewa an kashe sojojin tabbatar da zaman lafiya uku a tsakiyar daren jaumma'an da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran Spotnic ta nakalto ma'aikatar tsaron tana wannan bayanin a yau Lahadi, ta kuma kara da cewa wasu yan bindaga ne suka kaiwa sojojin hari a lokacinda suke kan hanyarsu ta tafiya hotu.

Ma'aikatar da kara da cewa tuni jami'an tsaron sun sami nasarar kama wadanda suka kai harin, sannan nan ba da dadewa ba za'a gurfanar da su a gaban kotu. 

Majalisar dinkin duniya tana da sojoji dubu 12,500 a kasar Mali wadanda suke kokarin tabbatar da zaman lafiya a arewacin kasar tun shekara ta 2013. Ya zuwa yanzu dai an kashi sojoji 190 daga cikin dakarun na Majalisar dinkin duniya.  

Tags