Feb 25, 2019 15:04 UTC
  • Sojojin Somalia Sun Kwace Iko Da Wasu Kauyuka Daga Hannun Alshabab

Dakarun kasar Somalia sun samu nasarar kwace wasu kauyuka biyu daga hannun mayakan ‘yan ta’addan Al-shabab.

Kamfanin dillancin labaran anatoli ya bayar da rahoton cewa, a yau dakarun kasar Somalia sun sanar da samu nasarar kwace wasu kauyuka biyu wato Hawa Adniyu da Gad Dufar daga hannun mayakan ‘yan ta’addan Al-shabab da suke iko da su tsawon lokaci.

Muhammad Abdullah kakain rundunar sojin Somalia ya bayyana cewa, Mayakan kungiyar ta Al-shabab sun janye da kansu a lokacin da suka ga rundunar sojin Somalia ta tunkaro yankin da wadannan kauyuka suke, inda suka fice ba tare da wani artabu ba.

Ya kara da cewa mayakan Al-shabab sun kasa yin tsayin daka a gaban sojojin Somalia a wadannan kayuka, a kan haka suka yanke shawarar arcewa ba tare da wata musayar wuta ba.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tags