Feb 28, 2019 06:21 UTC
  • Mali : An Kashe Fararen Hula 17

Majiyar tsaron kasar Mali ta sanar da kisan fararen hula 17 a tsakiyar kasar

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto majiyar tsaron kasar Mali a wannan laraba na cewa tashin Bam  da aka dasa a wani wurin taruwar jama'a ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 17 a tsakiyar kasar

Tun a shekarar 2012 ne kasar Mali dake yammacin Afirka ke fuskantar matsalar tsaro, bayan juyin mulki da sojoji suka yi, lamarin da ya sanya 'yan tawayen Abzunawa na kungiyar Azawad da wasu kungiyoyi masu tsaurin akida suka mamaye arewacin kasar.

A shekarar 2013, kasar Faransa da wasu kasashen Afirka sun tura dakarunsu zuwa kasar Ta Mali, inda suka kwato yankunan da aka mamaye, to amma duk da yawan dakarun kasashen wajen da aka jibge a kasar ta Mali, har ya zuwa yanzu, sun kasa kawo karshen matsalar tsaron da kasar take fuskanta.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a shekarar 2018 din da ta gabata sama da fararen hula 500 ne suka rasa rayukansu musaman ma a rikicin tsakiyar kasar ta Mali.

 

Tags