Feb 28, 2019 18:35 UTC
  • Akalla Mutane 20 Ne Suka Rasa Rayukansu A Hatsarin Jirgin Kasa A Birnin Alkahira

Mutane akalla 20 aka tabbatar da mutuwarsu da kuma wasu 43 da suka ji rauni sanadiyar hatsarin jirgin kasa da kuma gobarar da ta biyo baya a wata tashar jiragen kasa a birnin Alkahira na kasar Masar a jiya Laraba.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa hatsarin ya aukune saboda kuskuren matukin jirgin, wanda ya maida hankalinsa wani wuri har saida jirgin ya je ya Burma kan wasu gine-ginen da aka yi a tashar jiragen kasar, sannan daga baya, man disel da ke cikin jirgin ya kama da wuta.

Majiyar ma’aikatar shari’a ta kasar Masar ta bayyana cewa hotunan da nu’urar daukar hoto da ke tashar jiragen kasa ta Ramses tan an cewa matukin jirgin yana zantawa da wani har ya ji ya yi hatsari, kuma tuni yana hannun jami’an tsaro don amsa tambayoyi.

Ministan sifiri na kasar Hisham Arafat, ya ce gobaran da ta taso bayan hatsarin ya yi sanadiyyar motane a kalla 20, a tashar jiragen kasa na Ramses. Sannan gawakin wasunsu sun kone ta yadda baza’a iya tantancesu ba sai ta DNA. Labaran sun kara da cewa ministan sifirin ya ajiye aikinsa a jiya saboda wannan hatsarin da kuma asarar rayukan da aka yi.

 

Tags