Mar 03, 2019 07:35 UTC
  • Aljeriya : Buteflika Ya Kori Daraktan Kamfe Dinsa

Shugaba Abdelaziz Bouteflika, na Aljeriya, ya kori daraktan yakin neman zabensa, kana tsohon firaministansa Abdelmalek Sellal.

Kamfanin dilancin labaren Aljeriyana  APS, ya rawaito cewa tuni aka maye gurbin Mista  Sellal da Abdelghani Zaalane, wanda shi ne mnistan sufuri na kasar a yanzu.

Babu dai karin bayani akan dalilin korar shugaban yakin neaman zaben na shugaban kasar, amma dai matakin na zuwa ne a daidai lokacin da zanga zangar kin jinin sake tsayawa takarar Buteflika a wani wa'adin mulki na biyar ke kara bazuwa a kasar ta Aljeriya.

Wannan dai kusan shi ne matakin farko farko da ake ganin gwamnatin mai ci ta dauka tun daga lokacin da zanga zangar ta fara azuwa a kasar ta Aljeriya.

Dubban mutanen kasar Aljeriya ne suka gudanar da Zanga-zangar nuna kin amincewa da sake tsayawar takarar shugabanci na Abdulaziz Buteflika mai shekaru 82 dake mulkin kasar tun a 1999.

Zanga-zangar ranar Juma’a da ta gabata ita ce mafi girma wacce aka yi a  kasar ta Aljeriya da take yin kira ga shugaba Butaflika da ya kwashe shekara 20 kan madafun iko da kada ya sake tsayawa takarar shugancin kasar a karo na biyar.

 

 

 

Tags