Mar 04, 2019 04:48 UTC
  • Abdulaziz Butaflika Ya Zama Dan Takarar Shugaban Kasar A Algeriya Duk Tare Da Korafin Mutanen Kasar.

Shugaba Abdul Aziz Butaflika na kasar Algeriya ya sake zama dan takarar neman kujerar shugabancin kasar karo na biyar duk tare da korafe-korafen mutanen kasar dangane da hakan.

Kafafen yada labarai na kasar ta Aljeriya sun bayyana cewa a ranar Asabar da ta gabata ne Amdul-ghani Za'alan shugaban komitin yakin sake neman zaben shugaban kasar karo na ukku ya kaiwa majalisar kare kundinn tsarin mulkin kasar wacce take rijistan yan takarar shugaban kasa a kasar.

Za'alan ya mika takardun neman takarar shugabancin kasar na shugaba Butaflika ne jim kadan bayan dawowar shugaban daga wata tafiya gajeruwa da ya yi zuwa birnin Geneva na kasar Swizland don jinya.

Shugaban na kasar Aljeriya Abdul Aziz Butaflika dan shekara 82 a duniya yana shugabancin kasar Akgeriya ne tun shekara ta 1999, kuma an zabe shi a kan wannan kujerar har sau 4, duk da cewa a fili yake bai da lafiya. 

Tags