Mar 05, 2019 17:49 UTC
  • Kungiyar Da'esh A Yammacin Afirka Ta Kori Shugabanta Al'Barnawi

Kungiyar ‘Yan Ta’adda Ta “Daular Musulunci A Yammacin Afirka” Ta Kori Shugabanta Al Barnawi.

Dan jaridar nan mai sako labarai daga kungiyoyin ‘yan ta’adda a Najeriya, Ahmad Salkida ya ce; wani faifain nadaddiyar Magana ya bayyana yadda kungiyar ta Is ( Da’esh) ta sanar da nada Abdullahi Ibn Umar Al Barnawi a matsayin sabon shugaban kungiyar ta ‘yan ta’adda a yammacin Afirka.

Ahmad Salkida ya bayyana cewa; Shugaban kungiyar IS   ( “Da’esh) na duniya, Abubakar Bagadadi ne ya nada sabon shugaban kungiyar a yammacin Afirka.

Rahoton ya kuma ce babu wani cikakken dalili da aka bayyana na cire Abu Mus’ab amma dai har yanzu yana a tare da kungiyar ta ‘yan ta’adda yana kuna cigaba da yin aiki da ita.

A cikin watan Agusta na 2016 ne dai kungiyar ta Da’esh, ( ISIS) ta sanar da nadin Abu Mus’ab a matsayin shugabanta a yammacin Afirka.

Nadin nasa ya zo ne a wani yunkuri na uwar kungiyar ta ‘yan ta’adda na mayar da Abubakar Shekau saniyar ware

Tags