Mar 07, 2019 04:38 UTC
  • Nijar : An Dage Haramcin Kamun Kifi, Da Noman Tattasai Da Kasuwancinsa A Diffa

Gwamnatin Nijar, ta sanar da dage haramcin kamun kifi, da noman tattasai da kuma kasuwancinsa a jihar Diffa.

Matakin dai a cewar gwamnatin ya biyo bayan samun daidaituwar al'ammura a jihar ta Diffa dake fama da matsalar Boko Haram, akmar yadda wani babban jami'in ma'aikatar cikin gidan kasar ya sanarwa da kamfanin dilancin labaren AFP.

Saidai gwamnatin ta ce za'a dinga takan tsantsan akan saye da sayarwa na man fetur, da takin gona wanda har yanzu dai sai an nemi izinin mahukunta.

Yau Shekaru hudu kenan da gwamnatin ta dauki matakin, saboda a cewarta yadda 'yan boko haram ke amfanuwa da kudade na noman tattasan da kuma kasuwancinsa.

Matakin gwamnatin dai a cen baya ya jefa al'ummar jihar cikin kakani-kayi saboda dayewa daga cikin mutanen yankin na dogaro ne da noman tattasai, kasuwancinsa da kuma kamun kifi.

Jihar Diffa dai na karkashin dokar ta baci saboda matsalar ta boko haram.

Tags