Mar 09, 2019 04:12 UTC
  • © RYAD KRAMDI / AFP
    © RYAD KRAMDI / AFP

A Aljeriya, zanga zangar adawa da sake tsayawa takarar shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika, na ci gaba da bazuwa a kasar.

A jiya Juma'a ma dubun dubatar 'yan aksar ne suka gudanar da zanga zanga a biranen da suka hada da Algiers, Oran da Constantine.

Daga cikin wadanda suka halarci zanga zangar ta jya harda 'yan majalisar dokoki na jam'iyyar FLN, dake shugabancin kasar tun cikin shekara 1962.

Rahotanni daga kasar sun ce an samu fitowar jama'a sosai a zanga zangar, wanda ya kai har ga jami'an 'yan sanda sukayi amfani da hayaki mai sa hawaye don tawartsa masu zanga zangar dake kokarin kaiwa ga wata hanya dake kaiwa fadar shugaban kasar.

'Yan sanda a kasar sun ce sun cafke mutum 195 boyo bayan dauki-ba dadin da akayi tsakaninsu da masu zanga zangar.

Jami'an tsaro 112 ne aka rawaito cewa sun raunana a artabun da sukayi da masu zanga zangar.

.

Tags