Mar 09, 2019 04:20 UTC
  • Nijar : An Kori Gwamnan Jihar Diffa

Gwmanatin Nijar ta sanar da korar gwamnan jihar Diffa, Mal. Mahamadu Bakabe daga bakin aikinsa.

Gwamnatin ta sanar da hakan ne a yayin taron majalisar ministocinta na mako mako a jiya Juma'a.

Tuni gwamnatin ta maye gurbinsa da Injiniyan ruwa da gandun daji Mohamed Mouddour.

Sanarwar bata yi karin bayyani ba kan sallamar gwamnan jihar na Diffa, saidai hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan ya sanar da murabus dinsa tun kafin sanar da matakinn gwamnatin.

Wasu rahotanni sun ce ana zargin gwamnan da rashin tafiyarda harkokin kudi yadda ya kamata, musamman kudaden tallafi na kungiyoyn agaji, a jihar dake fama da matsalar Boko haram.

Tags