Mar 10, 2019 08:30 UTC
  • Boko Haram Ta kashe Sojin Nijar 7 A Diffa

Ma'aikatar tsaro a Nijar ta sanar da mutuwar sojojinta bakwai a wani hari da mayakan boko haram suka kai a kudu maso gabshin kasar.

Sanarwar ta kuma ce dakarun sun kashe mayakan na boko haram 38 da kuma cafke guda daga cikinsu.

Haka kuma sojojin sunyi nasarar kwato motocin maharan guda biyar da kuma bindigigi da dama da suka hada da AK47 guda huhu da makamin harba roka RPG guda biyu da kuma harsashai masu yawa iri daban daban.

Da yammacin ranar Juma'a data gabata ne maharan suka kai harin a kauyen Wulwa dake kusa da garin Gueskerou a jihar ta Diffa.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da kungiyar ta Boko haram ke kai hari kan jami'an tsaro na NIjar a wannan yankin na Diffa, inda ko a ranar 16 ga watan Fabrairu da ya gabata, wani hari makamancin wannan ya yi ajalin sojin kasar guda bakwai a garin Chetima Wangu a kudancin tafkin Chadi.

Tags