Mar 10, 2019 10:04 UTC
  • Buhari Ya Mayar Da Martani Ga Shirin Atiku Na Kai Kara Kotu

A karon farko shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya mayar da martani ga shirin dan takarar jam’iyyar PDP da ya sha kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar a kwanakin baya Alhaji Atiku Abubakar yana mai cewa hakan bai ba shi mamaki ba.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ya kada kuri’arsa a zaben gwamna da na ‘yan majalisun jihohi da aka gudanar a mazabarsa ta Kofar Baru III, Gidan Niyam da ke garin Daura na jihar Katsina inda yace bai yi mamakin maganar Atiku Abubakar din ba, yana mai cewa daman yana tsammanin hakan.

Dangane da batun matsalar tsaro da aka fuskantar a yayin zaben shugaban kasar da aka gudanar kuwa, shugaba Buhari ya bayyana damuwarsa kan hakan sai dai ya ce ya bar lamarin a hannun jami’an tsaron kasar musamman ‘yan sanda wadanda yace ya san sun san abin da ya kamata su yi.

Tun dai bayan da aka sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da sanar da shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben ne, Atiku Abubakar ya sha alkawarin kalubalantar sakamakon a kotu.

Tags

Ra'ayi