Mar 11, 2019 04:42 UTC
  • Najeriya : Ana Ci Gaba Fitar Da Sakamakon Zaben Gwamnoni

A Najeriya a yayin da ake ci gaba da fiatar da sakamakon zaben gwamnonin jihohin kasar, rahotanni daga kasar na cewa Jam’iyyar PDP ce ke kan gaba a jihohin Kano da kuma Bauchi.

Bayanai sun ce PDP ta yi nasara a Zaben gwamna da aka yi a Jihar Bauchi inda ta kada APC da gwamna mai ci Abubakar Mohammed.

A Sakamakon zaben da malamin Zaben gwamna na Jihar Bauchi ya bayyana a garin Bauchi, Sanata Bala Mohammed, Kauran Bauchi na Jam’iyyar PDP ne ya lashe Zaben da kuri’u 469,512, Inda gwamna mai ci na Jam’iyyar APC ya samu kuri’u 465,453.

Sai dai hukumar Zabe ta bayyana cewa wannan Zabe bai Kammala ba domin kuwa ba a bayyana sakamakon Zaben karamar Hukumar Tafawa Balewa ba.

A cen kuwa jihar Kano, inda nan ne zaben ya fi daukan hankali, sakamakon kawo yanzu na cewa PDP ce kan gaba da kuri'u 951,531 sai kuma APC dake da 935451.

Cen kuwa jihar Filato, hukumar zaben yankin ta ce zaben bai kammalu ba.

Tags

Ra'ayi