Mar 11, 2019 15:05 UTC
  • Sojojin Masar Sun Halaka 'yan Ta'adda 46

Rundunar sojin kasar Masar ta sanar da halaka 'yan ta'adda 46 a cikin yankin Sinai ta arewa.

KIamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a cikin wata sanarwa da rundunar sojin kasar Masar ta fitar a yau, ta sanar da cewa, dakarun kasar sun kadamar da wani farmaki a yankin Sinai ta arewa a kan wasu wuraren buyar 'yan ta'adda, kuma sun kashe adadi mai yawa daga cikinsu.

Bayanin ya kara da cewa, an yi musayar wuta tsakanin sojojin da kuma 'yan ta'adda masu alaka da kungiyar Daesh, inda bayan kashe 46 daga cikin 'yan ta'addan, a daya bangaren kuma sojoji 3 sun rasa rayukansu.

Tun bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Masar Muhammad Morsi ne dai aka samu bullar kungiyoyi masu dauke da makamai masu da'awar jihadi a yankin Sinai ta arewa, inda suke kai hare-hare kan jami'an tsaro da kuma wurare ibada na mabiya addinin kirista.

 

Tags