Mar 12, 2019 05:42 UTC
  • Aljeriya: Butaflika Ya janye Daga Takarar Shugabancin Kasa

Shugaban kasar Aljeriya ya janye daga takarar neman shugabancin kasar a wani wa'adi na biyar.

Kamfanin dilalncin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, shugaban kasar Aljeriya Abdulaziz Butaflika ya sanar da cewa ya janye daga takarar neman shugabancin kasar a wani sabon wa'adin mulki karo na biyar, kuma ya dage gudanar da zabukan da aka shirya gudanar a a ranar 18 ga watan Afirilun wanann shekara.

Shugaba Butaflika ya sanar da hakan nea  cikin wani dogon sako da ya fitar, inda ya ce kasar Aljeriya tana cikin wani yanayi da ya kamata a yi la'akari da shi, kuma ya yaba da yadda al'ummar kasar suka bayyana ra'ayinsu ta hanyoyin gangami na lumana, wanda a cewarsa wannan babban abin yabawa ne.

Ya ce ya yanke wananns hawara ne saboda bukatar da 'yan kasa suka gabatar masa, kuma a kowane lokaci yana tare da ra'ayin al'ummar Aljeriya.

Tun daga ranar 22 ga watan Fabrarirun da ya gabata ne aka fara gudanar da zanga-zangar nuna kin amincewa da takarar Butaflika dan shekaru 82 da ke fama da rashin lafiya.

 

Tags