Mar 14, 2019 09:04 UTC
  • Najeriya : Buhari Ya Jajantawa Iyayen Yaran Da Suka Mutu A Ruftawar Gini

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin dadi sakamakon ruftawar wani bene mai hawa uku na wata makarantar firamare a yankin Ita-Faji dake jahar Legas, wanda yayi ajalin yara ‘yan makaranta da dama.

A wata sanarwa da aka fitar a Abuja, shugaba Buhari ya jajantawa iyayen yara da dangin wadanda hadarin ya rutsa da su kana ya yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka samu raunuka.

Shugaban kasar ya bukaci gwamnatin jahar Legas, da ta dauki dukkan matakan da suka dace domin kaucewa afkuwar irin hakan a nan gaba.

Alkaluma na baya-bayan nan na nuni da cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya kai 18 sakamakon ruftawar ginin a birnin Legas da ke kudun maso yammacin Najeriya, yayin da wasu akalla 41 suka samu raunuka.

Tags