Mar 16, 2019 12:29 UTC
  • Maganin mai suna \'\'Mencevax ACWY\'\', an rubuta kansa cewa anyi shi a watan Disamba na 2016, kuma lokacin aiki dashi zai kare a Nowamba na 2021.
    Maganin mai suna \'\'Mencevax ACWY\'\', an rubuta kansa cewa anyi shi a watan Disamba na 2016, kuma lokacin aiki dashi zai kare a Nowamba na 2021.

Hukumomi a Nijar, sun ja hankalin masu ruwa da tsaki kan harkar kiwan lafiya da kuma jama'a, biyo bayan gano wani maganin alura na bogi na cutar sankarau a kasar.

A jiya Juma'a ne hukumomin kiwan lafiya na kasar, suka sanar da cewa sun gano wani nau'in maganin cutar ta sankarau na alura, bayan wani bincike da kwararu na ma'aikatar suka gudanar.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta kaddamar a ranar 5 ga watan Maris da kamfe na shaushawar riga kafin cutar ta sankarau, domin kare milyoyin mutane musamman yara daga kamuwa da cutar mai yaduwa da kuma kisa.

A cikin sanarwar data fitar, ma'aikatar lafiya ta kasar, ta bukaci ma'aikatan lafiya da suyi taka tsan-tsan akan nau'in maganin na alura mai suna ''Mencevax ACWY'', wanda aka rubuta kansa cewa anyi shi a watan Disamba na 2016, kuma lokacin aiki dashi zai kare a Nowamba na 2021.

A shekara 2018, hukumomin kiwan lafiya na Nijar, sun rufe gomman cibiyoyi masu shigo da magunguna masu zaman kansu dake sayar da magunguna wadanda suka lalace ko dai kuma ake da shakku akansu a Yamai babban birnin kasar.

Tags