Mar 17, 2019 05:35 UTC
  • Zimbabwe: Mutane 115 Ne Ake Sa Ran Sun Rasa Rayukansu A Wata Guguwar Iska

Gwamnatin kasar Zimbabwe ta sanar da cewa akalla mutane 115 ne ake sa ran sun rasa rayukansu a wata guguwar Iska da ta taso a yankunan gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, ma'aikatar yada labaran kasar Zimbabwe ta sanara  jiya Asabar cewa, bayan da wata guguwar mai karfi ta taso a  jiya a gabashin kasar, hakan ya haddasa barna da kuma asarar rayukan jama'a.

Bayanin ya ce an samu gawawwakin mutane 15 da suka mutu  sakamakon hakan, yayin da kuma guguwar ta tafi da mutane akalla 100, wadanda babu duriyarsu.

A kasar Zimbabwe dai a kan fuskanci matsaloli na guguwar iska da kuma ambaliyar ruwa a wasu lokuta, wanda kan yi sanadiyyar mutuwar mutane, da kuma jawo a asarar dukiyoyi masu tarin yawa, musammana  kan amfanin gona.

Tags