Mar 17, 2019 18:39 UTC
  • 'Yan Bindiga Sun Kashe Sojojin Mali 16

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari akan wani sansanin sojan Mali da yake a tsakiyar kasar tare da kashe sojoji 16.

Babban jami’in gwamnati a yankin da lamarin ya faru, ya shaidawa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa; “Yan bindigar sun kuma kwace iko da barikin sojan a yau Lahadi.

Majiyar ta kara da cewa; Maharan sun kuma kone barikin sojan kurmus sannan kuma sun yi a won gaba da makamai.

Kasar ta Mali dai tana fama da masu dauke da makamai a cikin tsakiyar kasar da kuma arewacinta.

Majiyar tsaron kasar ta Mali ta danganta harin da na kungiyar masu tsaurin ra’ayi ta Jama’at Nusra al-Islam, wacce wani reshe ne na kungiyar Al-Qaeda a yammacin Afrika.

Tags