Mar 17, 2019 18:46 UTC
  • Sudan : Al-Bashir Ya Yi Fatan Inganta Huldar Kasarsa Da Rasha

Shugaba Omar al-Bashir na kasar Sudan ya bayyana fatansa na inganta huldar dake tsakanin kasarsa da kuma kasar Rasha.

Shugaban Sudan ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da Mikhail Bogdanov, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha kuma wakilin musamman kan batun yankin Gabas ta Tsakiya a wannan a  Khartoum, babban birnin kasar.

Bisa sanarwar da fadar shugaban kasar Sudan ta bayar, an ce, a yayin ganawar, shugaba al-Bashir ya ce, inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu a fannonin siyasa, tattalin arziki da cinikayya ya dace da moriyarsu duka.

Mista Mikhail Bogdanov, ya yiwa kafofin yada labaru bayani bayan ganawar cewa, bangarorin biyu sun tattauna hadin gwiwar dake tsakanin Rasha da Sudan ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, da kuma baiwa jami'an Sudan horo da makamantansu.

 

Tags