Mar 18, 2019 05:25 UTC
  • Aljeriya : AU Ta Jinjina Wa Bouteflika Kan Janye Takararsa

Kungiyar tarayya Afirka (AU) ta yi kira ga bangarori a Aljeriya dasu tattaunada juna domin cimma daidaito akan matakin da shugaban kasar ya dauka na janye wa daga takara shugaban kasa a karo na biyar.

Wannan dai shi ne karon farko da kungiyar ta (AU), ta yi bayyani tun bayan zanga zangar kin jinin sake tsayawa takara shugaban kasar ta Aljeriya mai shekaru 82 a karo na biyar.

A cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin kungiyar Musa Faki Mahamat ya sanya wa hannu, kungiyar ta AU, ta jinjinawa shugaba Butaflika akan matakin da ya dauka.

Sanarwar ta ce kungiyar tarayya ta Afrika na ci gaba da bibiyar al'amuran dake faruwa a kasar ta Aljeriya, tare da yabawa da halayen mutanen kasar dake zanga zanga cikin lumana.

Kiran kungiyar ta AU na zuwa ne a daidai lokacin da zanga zangar da ake a kasar ta ALjeriya ke ci gaba da bazuwa duk da shugaban kasar ya janye anniyarsa ta sake tsayawa takara, saidai ba tare da bayyana ranar da za'a je zaben shugaban kasar ba.

Ko a ranar Juma'a data gabata ma, dubun dubatar 'yan kasar ne suka fito zanga zanga a biranen da suka hada da Alger, Oran, Tizi Ouzou, Constantine da kuma Annaba.

 

Tags