Mar 18, 2019 05:29 UTC
  • Nijar Da Rasha Zasu Karfafa Alaka Ta Fuskar Tsaro Da Ci Gaba

Kasashen Nijar da Rasha sun yunkuri anniyar farfado da huldar dake tsakaninsu da zumar karfafa hulda ta fuskar tsaro da kuma ci gaba.

Kasashen sun bayyana hakan ne bayan wata ganawa da shugaba Isufu Mahamdu ya yi da jakadan Rasha a kasar .Alexey Doulian.

Da yake karin bayyani ga manema labarai bayan ganawar jakadan na Rasha M. Doulian, ya ce ya gana da shugaba Isufu ne don mika masa da gayatar takwaransa na Rasha Vladimir Putin, ta taron kasashen Afrika da Rasha da za'a gudanar da watan Oktoba na wannan shekara a birnin Sotchi.

Jakadan na Rasha ya ce ya ji dadi matuka akan yadda shugaba Isufu na NIjar, ya amsa goron gayyatar taron, da kuma yadda Nijar din ta ce zata bude ofishin jakadancinta a birnin Moscow domin karfafa alaka ta diflomatsiyya da Rashar.

 

Tags