Mar 18, 2019 11:58 UTC
  • Tashin Bama-Bamai Ya Yi Ajalin Sojin Burkina Faso 5

A Burkina Faso, sojojin kasar biyar ne suka rasa rayukansu a wasu jerin tashin bama-bamai kirar gargajiya a gabashin kasar.

Lamarin dai ya faru ne tsakanin ranakun Asabar zuwa Lahadi a yankin Kompienga dake gabashin kasar, kamar yadda wata majiyar tsaro ta shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP.

Majiyar ta ce da yammacin jiya Lahadi, wani bam ya tashi da wata motar soji, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji guda uku da kuma raunata guda.

Kafin hakan kuma a ranar Asabar, irin hakan ta faru inda wata motar sojin ta taka wani abu mai fashewa, inda kuma nan wani soja guda da wani jami'in tsaron Jandarma suka rasa rayukansu.

A farkon watan Maris din nan sojojin aksar ta Burkina Faso, suka kaddamar da farmaki mai manufar kakkabe yankin gabashin kasar da kuma tsakiya daga duk wata barzanar 'yan tada kayar baya da 'yan ta'adda.

Tags