Mar 18, 2019 12:52 UTC
  • D.R Congo : Mutum 32 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Kasa

A Jamhuriya Demokuradiyyar Congo, mutane akalla 32 ne suka rasa rayukansu, kana wasu 91 suka raunana a lokacin da wani jirgin kasa ya kaucewa hanyarsa.

Daga cikin wadanda suka rauna akwai 18 dake cikin mayuyacin hali.

Bayanai daga kasar sun ce mafi yawa daga cikin wadanda lamarin ya rusa dasu yara ne.

Hatsarin na yau Lahadi, ya auku ne a yankin Kasaï, inda taragai da dama suka jirkice suka fada cikin wani kogin yankin.

"yan sanda a yankin sun ce akwai taragai na jirgin kasan da dama da suka fada a kogi, wadanda kuma ba'a san ko akwai mutane ciki ba ko a'a.

Wannan dai shi ne hastarin jirgin kasa na uku a cikin wata guda a tsakiyar wannan kasa ta Jamhuriya Demokuradiyyar Congo.

Kwararu kan harkar sufiri na danganta hatsarurukan jiragen kasa da ake samu a kasar da tsufar jiragen kasan, kasancewar mafi yawansu kirar shekarar 1960 ne.

Tags