Mar 19, 2019 09:52 UTC
  • Sudan Da Sudan Ta Kudu Sun Cimma Matsaya Na Bude Iyakokinsu

Kwamitin hadin gwiwar tsaro da Siyasa na kasashen Sudan da Sudan Ta Kudu sun cimma matsaya na bude iyakokin kasashen biyu.

Rahotani dake fitowa daga kasar Sudan sun ce a jiya Litinin, kwamitin hadin gwiwar da aka kafa tsakanin kasar da kasar Sudan ta kudu kan harakokin da suka shafi tsaro da siyasa sun sanya hanu kan yarjejjeniyar da suka cimma na sake bude iyakokin kasashen biyu.

Wannan mataki na zuwa ne, kwana guda, bayan cimma yarjejjeniyar shata iyakokin kasashen biyu a  birnin Adis Ababa fadar milkin kasar Habasha.

A cewar Kamal Abdul-Ma'aruf shugaban rundunar tsaron hadin gwiwa na kasar Sudan ya ce sun cimma yarjejjeniyar samar da wani yanki na tsaro a kan iyakokin kasashen biyu, inda dukkanin kasashe za su kwashe jami'an tsaron su, sannar kuma a tura wata tawagar hadin gwiwa bisa sa idon MDD zuwa yankin Abyei domin samun tabbaci na fitar jami'an tsaron kasashen biyu daga yankin.

Tun a ranar 27 na watan Satumbar 2012 ne, kasashen biyu suka sanya hanu kan wata yarjejjeniyar tushe duk wata hanya na aikewa da makamai zuwa ga 'yan tawayen kasashen biyu.

Bisa sabuwar yarjejjeniyar da aka cimma tsakanin kasashen biyu za su samar da wani yankin na tsaro mai tsahon kilomita 10.

Tags