Mar 24, 2019 03:27 UTC
  • Ali Bongo Ya Koma Gabadaya A Gabon

Shugaba Ali Bongo na Gabon, ya koma kasarsa baki daya bayan shafe watanni na jinya.

A yayin komawarsa gida, Shugaba Bongo, ya samu kyaukyawar tarba daga jama'ar kasar.

Tun dai bayan da ya kamu da bugun zuciya wanda ya haifar masa da shanyewar wani bangare na jiki, sau biyu kawai Ali Bongo ya je kasarsa a cikin watanni biyar.

Tun bayan da ya kamu da rashin lafiyar, wannan shi ne karo na farko da ya yi fitowa harma ya yi tataki a bainar jama'a.

Tun bayan da ya kamu da rashin lafiya, ba'a cika samun bayyanai ba akan ainahin rashin lafiyar tasa ko kuma halin da yake ciki.

A yayin da Shugaba Bongo ke son kammala wa'adin mulkinsa na biyu, wasu kungiyoyin fara hula da na 'yan adawa na ci gaba da bukatar ganin an gudanar da bincike marar bangarenci kan rashin lafiyar shugaban domin tantance ko zai iya mulkin kasar.

Tags