Mar 24, 2019 03:43 UTC
  • Chadi : Deby, Ya Kori Manyan Sojoji, Bayan Harin Boko Haram

Shugaba Idriss Deby na kasar Chadi, ya kori babban hafsan sojin kasar, Brahim Seid Mahamat, bayan shafe shekaru shida yana rike da wannan mukami.

An dai maye gurbinsa da Janar Taher Erda, wanda shi ne babban kwamandan rundinar sojin kasa.

Babu dai karin bayyanin da akayi akan dalilin wannan canjin a koluluwar rundinar sojin kasar.

Saidai wannan canjin na zuwa ne, a kasa da sa'o'i 24 bayan wani harin Boko haram da ya yi sanadin mutuwar sojojin kasar ta Chadi 23 a kudu maso yammacin kasar.

Wasu majiyoyi sun ce an kori babban hafsan sojin kasar ne, bayan mutuwar sojojin kasar 23, da kuma ta wasu sojin kasar hudu da aka gano gawarwakinsu a wani jirgin mai saukar ungulu a arewacin kasar.

An dai gano gawarwakin sojojin ne kwanaki goma bayan da suka bata.

Ko baya ga babban hafsan sojin kasar, shugaba Deby ya kori wasu manyan sojoji da suka hada dana bangaren soji a fadar shugaban kasar. sannan kuma ya kori babban hafsan sojin sama na kasar da kuma mukadashinsa a ecwar kamfanin dilnacin labaren France-Presse.

Harin dai wanda aka kai a cikin daren ranar Alhamis data gabata shi ne irinsa mafi muni da aka kaiwa sojin kasar ta Chadi a yakin da suke da kungiyar Boko Haram.

Tags