Mar 24, 2019 05:17 UTC
  • Sudan : Wani Abun Fashewa Ya Yi Ajalin Yara 8

'Yan sanda a Sudan sun ce yara takwas ne suka rasa rayukansu, biyo bayan fashewar wani abu da ba'a kai ga tantance ko minene ba, a yankin Omdourman.

Bayanai sun ce yaran da lamarin ya rusa dasu, masu tsutar karafa ne na saudawa, kuma sun rasu ne bayan da suka tsinci wani karfe wanda bsia ga dukkan alamu suka nemi fasawa, nan ne kuma abun ya tarwatse.

Bakwai daga cikin yaran sun mutu nan take, sai kuma guda da ya cika a asibiti.

Rahotanni sun ce yankin na lamarin ya faru, ya taba kasancewa wirin atisayen sojoji a wasu shekaru da suka gabata.

Tags