Aug 22, 2018 06:29 UTC
  • Ayatullahi Khatami Ya Ce: Duk Wani Yaki Da Amurka Zata Kaddamar Kan Iran Zai Janyo Mata Babban Hasara

Limamin da ya jagoranci sallar idin lahiya a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran ya bayyana cewa: Duk wani yaki da kasar Amurka zata kaddamar kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yakin zai shafi babbar 'yar lelan Amurka a yankin.

A hudubar sallar idi da ya gabatar a babban Masallacin birnin Tehran a yau Laraba: Ayatullahi Ahmad Khatami ya fayyace cewa: Babu wanda ya zai iya kwatanta irin hasarar da za a yi a duk wani yakin da kasar Amurka zata yi gigin kaddamarwa kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran saboda Iran zata dauki matakin maida martani da zai kaskanta Amurka da kawayenta musamman haramtacciyar kasar Isra'ila.

Ayatullahi Khatami ya kara da cewa: Al'ummar Iran a tsawon shekaru kimanin 40 da suka gabata sun yi nasarar tilastawa makiyansu fitar da rai kan kasarsu, sannan ya fayyace salon makircin da makiya suke ci gaba da gudanarwa na raba kan al'ummar musulmin duniya tare da kunna wutan rikici a tsakanin musulmi da ke kai ga rasa rayukansu.

Har ila yau Ayatullahi Khatami ya tabo batun bayanin Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran cewa: Iran ba zata amince da duk wani zaman tattaunawa da kasar Amurka ba; Yana mai jaddada cewa: Tun bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran, Amurkawa suke kokarin ganin sun gudanar da zaman tattaunawa da Iran amma basu wannan damar ba, kuma ba zasu samu a nan gaba ba saboda sanin mummunan halinsu.   

Tags