Sep 08, 2018 18:55 UTC
  • Mahukunta A Kasar Iran Sun Zartar Da Hukuncin Kisa Kan 'Yan Ta'adda Uku A Shiyar Yammacin Kasar

Mahukuntan kasar Iran sun zartar da hukuncin kisa kan wasu 'yan ta'adda uku da aka tabbatar da laifinsu na kunna wutan rikici da aiwatar da ayyukan ta'addanci da suka lashe rayukan mutane hudu a shiyar yammacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran kasar Iran "IRNA" ya watsa rahoton cewa: A safiyar yau Asabar mahukuntan kasar Iran sun zartar da hukuncin kisa kan wasu 'yan ta'adda uku a garin Marivan da ke shiyar yammacin kasar bayan samunsu da laifin kunna wutan rikicin addini, aiwatar da kisan gilla da kuma hada baki da cibiyoyin leken asirin kasashen waje. 

'Yan ta'addan uku an basu damar kare kansu tare da samun tallafin lauyoyi masu kare su amma duk da haka kotu ta same su da laifuka kan zarge-zargen da ake yi kansu, kuma kotun kolin kasa ta amince da hukuncin da aka yanke kansu.

A ranar 23 ga watan Yunin shekara ta 2017 ne gungun 'yan ta'addan suka farma al'ummar Kurdawan kasar Iran da suke gudanar da zanga-zangar ranar Qudus ta Duniya, inda 'yan ta'addan suka bude wutan bindiga kan jama'a da tada bom gami da yin musayar wuta da jami'an tsaro, inda ayyukan ta'addancinsu ya lashe rayukan mutane hudu ciki har da dan babban limamin garin.  

Tags