Sep 09, 2018 07:30 UTC
  • An Zartar Da Hukuncin Kisa Kan Wasu 'Yan Ta'adda Uku A Yammacin Kasar Iran

An zartar da hukuncin kisan da wata kotu ta yanke wa wasu 'yan ta'adda guda uku sakamakon wani harin ta'addanci da suka kai yammacin kasar da yayi sanadiyyar shahadar wani adadi na mutanen gari.

Kamfanin dillancin labaran kasar Iran (IRNA) ya bayyana cewar an zartar da hukuncin kisan da aka yanke wa 'yan ta'addan ne bayan shari'ar da aka yi musu da kuma tabbatar da zargin da ake musu na shiga cikin kungiyar ta'addanci, amfani da makamai da kuma kai harin ta'addancin da yayi sanadiyyar mutuwar wasu mutane.

Daga cikin ayyukan ta'addancin da aka sami wadannan mutane ukun da aikatawa har da wani hari da suka kai garin Marivan da ke yammacin kasar ta Iran lamarin da yayi sanadiyyar shahadar mutane 4 ciki har da dan limamin juma'ar garin da nufin haifar da fitina ta mazhaba a garin.

Har ila yau daga cikin ayyukan da wadannan 'yan ta'addan suka aikata har da shiryawa da kuma hada baki da wasu kungiyoyin 'yan ta'adda da nufin tada bama-bamai da zubar da jinin fararen hula a Ranar Kudus ta shekarar da ta gabata a yankin Kurdawan kasar Iran bugu da kari kan kai hare-hare da makamai kan jami'an tsaro a ranar 23 ga watan Yunin 2017.

Tags