Sep 10, 2018 05:51 UTC
  • Qasemi: Dole Ne Gwamnatin Iraki Ta Hukunta Wadanda Suka Kai Harin Kan Ofishin Iran

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi ya kirayi gwamnatin Iraki da ta hukunta wadanda suka kai hari kan karamin jakadancin Iran da ke Basara.

A  lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a jiya a birnin Tehran, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi, ya bayyana harin da wasu mutane suka kai kan karamin ofishin jakadancin Iran da ke Basara da cewa lamari ne mai matukar hadari.

Ya ce babbar manufar hakan ita ce rusa kyakkayawar alakar da ke tsaanin Iran da Iraki, wanda kuma hakan babu wanda zai amfanar sai makiya al’ummomin kasashen biyu.

Qasemi ya ce kai hari kan ofishin na Iran a Basara ko alama ba abu ne da za a lamunta da shi ba, a kan ya ce dole ne gwamnatin Iraki ta dauki matakin gano wadanda suke da hannu a cikin lamarin domin hukunta su, kuma wajibi ne da ya rataya kan gwamnatin ta Iraki ta bayar da kariya ga jam’an diflomasiyya na Iran da kuma sauran wurare na diflomasiyyar kasar da ke cikin Iraki.

Tags