Oct 01, 2018 05:39 UTC
  • Iran Ta Yi Ruwan Makamai Masu Linzami Na Maida Martani Kan Harin Ahwaz

Dakarun kare juyin juya halin Musulinci na Jamhuriya Musulinci ta Iran, sun sanar da kai hare hare na makamai masu linzami kan wani babban sansanin 'yan ta'adda a gabashin Siriya, a matsayin maida martani kan harin da aka kai a birnin Ahwaz.

Sanarwar da bangaren tsaron sararin samaniya na rundinar ta IRGC, ya fitar ta ce, harin da aka kai da jijibin safiyar Litinin din nan da makamai masu linzami kirar ''sol-sol'' ya hallaka mayakan takfiriya masu yawa da kuma raunana da dama daga cikinsu ciki kuma harda wadanda suka kisa harin na ranar 22 ga watan Satumba da ya gabata a birnin Ahwaz.

An kai harin ne da makaman masu linzami guda shida, samfarin "Zulfikar da "Kiyam", kuma sun bi ta sararin samaniyar Iraki, kafin su aukawa babban sansanin 'yan ta'addan a yankin Deir ez-Zor, a cewar sanarwar.

Makamman masu linzami samfarin ""Zulfikar da "Kiyam" irin masu cin matsakaicin zango ne na kilomita 750 zuwa 800.

Harin ta'addancin dai na ranar 22 ga watan Satumba da aka kai a yayin wani faretin soji a garin na Ahwaz dake yankin Khouzistan a kudancin kasar ta Iran, ya dai yi sanadin shahadar mutane akalla 25 tare da raunana da dama.

Bayan harin dama Jamhuriya musulinci ta Iran ta sha alwashin maida martani mai tsanani kan duk wadanda suke da hannu wajen kisa harin da kuma masu daure masu gindi.

Iran dai ta dora alhakin kai harin ga kungiyar 'yan ta'addan nan ta ''Ahwaziya'' dake samun goyan bayan kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Tags