Oct 06, 2018 06:43 UTC
  • Babban Bankin Iran: Takunkuman Amurka Ba Za Su Yi Tasiri A Harkokin Kudi Na Kasr Ba.

Shugaban babban bankin Iran Abdunnasir Himmati ya ce takunkuman da gwamnatin Amurka ta dorawa kasar Iran ba zasu yi tasiri a cikin harkokin kudi na kasar Iran ba.

Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto Abdunnasir Himmati yana fadar haka a birnin Mosco na kasar Rasha a wani ziyarar aiki da ya fara a kasar a ranar laraban da ta gabata . Himmati ya kara da cewa a ganawarsa da Elvira Nabiullina shugaban babban bankin kasar Rasha bangarorin biyu sun amince su gudanar da harkokin kasuwanci a tsakaninsu da kudaden kasashensu kai tsaye ba tare da dalar Amurka ta shiga tsakani ba. 

Himmati ya kara da cewa a halin yanzu kimani kashi 30% na harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu suna gudana ne da kudaden kasashen biyu ba tare da shigar dalar Amurka ba. 

Daga karshe jami'in babban bankin na Iran ya kammala da cewa gwamnatin kasar Iran ta samar da wasu hanyoyi na sayar da danyen man fetur na kasar tare da wasu kasashen duniya ba tare da shigar dalar Amurka a tsakani ba. Don haka takunkumin amfani da kudaden Amurka wanda gwamnatin Shugaba Trump ta dorawa kasar ba zai yi wani tasiri a harkokin kudaden kasar ba.

 

Tags