Oct 18, 2018 05:51 UTC
  • Rasha Ta Mayar Da Kakkausan Martani Kan Sabbin Takunkuman Amurka A Kan Iran

Gwamnatin kasar Rasha ta mayar da martani da kakkausar murya dangane da sabbin takunkuman da Amurka ta sake kakaba wa kasar Iran.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Ryabkov ya bayyana cewa; irin wadannan matakan da Amurka take dauka a kan Iran sun yi hannun riga da dukkanin ka'idoji da dokoki na duniya, a kan haka Rasha ba taba amincewa da su ba.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Rasha ya kara da cewa, akwai matakai daban-daban na hadin gwiwa da kasashen Rasha da Iran za su dauka domin tunkarar wadannan takunkumai na Amurka.

Sabbin takunkuman na Amurka a kan kasar Iran dai sun shafi wasu kamfanoni da kuma wasu bankunan kasar, a cikin makon farkon watan Nuwamba mai kamawa ne kuma takunkumin Amurka kan sayar da danyen manfetur din kasar Iran zai fara aiki, inda Amurka ta ce tana son ganin cewa an kai matsayin  da Iran ba za ta iya sayar da ko ganga daya ta danyen manfetur ba.

Tags