Nov 05, 2018 19:08 UTC
  • Shirin Musayar Kudade Tsakanin Iran Da Tarayyar Turai Na Tafiya Yadda Yakamata

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bada sanarwan cewa shirin musayar kudade tsakanin Iran da kasashen tarayyar Turai na tafiya kamar yadda ya dace

Bahram Qasem,i kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ne ya bayyana haka a yau litinin, a lokacinda yake bayani wa kafafen yada labarai na ciki da wajen kasar.

Qasemi ya kara da cewa shirin musayar kudaden yana da muhimmanci, musamman bayan da Amurka ta dawo da takunkuman da ta dorawa kasar Iran na hanta sayar da danyen man fetur na kasar. 

Dangane da dawo da takunkumin kuma, Qasemi ya ce Amurka ce ta dorawa kanta takunkumi, don abinda ta yi ya sabawa dokokin kasa da kasa, banda haka kasashen duniya da dama basu amince da matakin da ta dauka ba. Har'ila yau bada izini ga wasu kasashe su ci gaba da sayan man fetur na kasar Iran , wanda gwamnatin Amurka ta yi, jada baya ne daga takunkumin.

 

Tags