Fiye Da Masu Zanga-zanga 300 Ne Jami'an Tsaro Su ka Kama A Kasar Faransa
Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ambato ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Faransa na cewa; Mutanen da aka kama sun kai 345, kuma ana ci gaba da tsare 281 daga cikinsu
A ranar asabar din da ta gabata mutane 50,000 ne su ka yi Zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin kasar ta Faransa a fadin kasar
Adadin masu Zanga-zangar ya karu idan aka kwatanta shi da na makwannin da su ka gabata
A ranar 17 ga wata Nuwamba ne dai al'ummar kasar ta Faransa su ka fara gudanar da Zanga-zangar nuna kin jinin tsarin jari-hujja. Zanga-zangar ta fara bayan da aka yi karin kudin makamashi
Tare da cewa an yi ganawa a tsakanin wakilan masu Zanga-zangar da ke sanye da tufafi ruwan dorawa, da kuma gwamnatin kasar, sai dai ba a kai ga cimma matsaya ba
Ya zuwa yanzu mutane 10 ne aka tabbatar da cewa sun mutu a sanadiyyar taho mu gama da jami'an tsaro