Jan 24, 2019 19:25 UTC
  • Gwamnatin Amurka Ta Kara Yawan Kamfanonin Kasar Iran Da Ta Dorawa Takunkuman Tattalin Arziki.

Ma'aikatar kudi ko baitul Malin Amurka ta bada sanarwan kara wasu kamfanonin jaragen sama mallalin iraniyawa cikin jerin wadanda ta dorawa takunkumi a yau Alhamis.

Kamfanin dillancin labaran Rauters ya nakalto ma'aikatar tana fadara haka a yau Alhamis. Kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu wadanda Amurkan ta kara a cikin jerin kamfanonin Iran da ta dorawa takunkuman dai sun hada da  Fars Air Qeshm da kuma  Flight Travel. 

Ma'aikatar kudi ta kasar Amurka ta kara da cewa daga yau ta haramta mu'amala da wadannan kamfanonin jiragen sama mallakin iraniya, kuma zata ladabtar da duk wanda ya sabawa haramcin. Daga karshe ma'aikatar ta kudi ta ce ta dorawa Iran wadannan takunkumai ne don abinda ta kira "tallafawa ayyukan ta'addanci a duniya". 

Gwamnatin kasar Amurka dai ta sha alwashin sai ta dorawa gwamnatin JMI takunkuman da ba'a taba dorowa wata kasa a duniya ba, don dunkusar da ita. 

A cikin watan Mayun shekara ta 2018 ne gwamnatin shugaba Donal Trump ta shelanta ficewar kasar daga yerjejeniyar Nukliyar kasar Iran ta shekara ta 2015. 

Sannan ta maida dukkan takunkuman da aka dorawa kasar kafin yerjejeniyar, a marhaloli biyu. Marhala ta farkon ya fara bayan watanni 3, sannan mafi tsananin kuma bayan watannin 6. Kuma sha alwashin hana kasashen duniya gaba daya sayan danyen man fetur na kasar Iran.  

gwamnatinn JMI ta bayyana cewa wadannan takunkuman ba zasu kai Amurka ga cimma burinta na ganin bayan Jumhuriyar Musulunci a Iran ba. 

Tags