Jan 25, 2019 19:16 UTC
  • Faransa Ta Bukaci Iran Ta Dakatar Da Shirinta Na Makamai Masu Linzami

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Faransa ta bada sanarwan cewa shirin makamai masu linzami na kasar Iran barazana ne gareta, don haka ne dole Iran ta dakatar da shirin ko kuma ta dora mata takunkumai masu tsanani

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar ta Faransa ya nakalto Jean -Yves Le Drian ministan harkokin wajen kasar ta Faransa ya na fadara haka a yau Jumma'a. Ya kuma kara da cewa shirin makamai masu linzami na bilistic barazana ce ga kasar Faransa don haka dole ne gwamnatin JMI ta dakatar da samar da irin wannan makamai ko kuma a dora mata tsakunkumai masu tsanani.

Jumhuriyar Musulunci ta Iran dai ta sha nanata cewa shirinta na makamai masu linzami baya barazana ga ko wace kasa a duniya sannan tana samar da irin wadannan makamai don kariya ne daga makiya kawai. Banda haka shirin nata bai sabawa kudurin MDD kan wannnan batun ba. 

Don haka gwamnatin JMI ba zata taba amincewa da dakatar da kare mutanen kasarta daga makiya ba. 

Tags