Feb 02, 2019 15:19 UTC

Iran ta sanar da harba wani makami mai linzami cikin nasara a yau Asabar, a daidai lokacin da kasar ta fara bukukuwan zagayowar ranakun cika shekaru arba'in cif da nasara yuyin juya halin musulinci na kasar.

Da yake sanar da hakan, ministan tsaron kasar, Janar Amir Hatami, ya ce an harba makamin samfarin ''Hoveyzeh'' cikin nasara, inda ya ci zango na kilomita 1.200 har ya kai inda aka bukata.

Ministan ya kimanta makamin ''Hoveizeh'' da babbar nasara ta kariya, da kuma hannu na garkuwa na Jamhuriya musulinci ta Iran.

A yayin bikin gabatar da makamin a yau, ministan tsaron kasar ta Iran, ya kara jadadda cewa, batun makaman kariya na Iran, batu wanda ba za'a taba amince tattaunawa akan shi ba, ko da hakan ba zata ma kowa dadi ba.

Janar din dai na maida martani kan kasashen yamma musamman Amurka da 'yan korenta da kuma wasu kasashen Turai dake son ganin Iran ta daina kera makamai kare kanta, a daidai lokacin da take fuskantar barazanar makiya.

Tags